Wa ke tallafawa 'yan ta'adda?

Hakkin mallakar hoto
Image caption 'Yan kungiyar IS suna samun kudade daga wurare da dama.

Ana yin wani taron koli a Sydney, babban birnin kasar Australiya domin gano hanyoyin samun kudaden 'yan ta'adda.

Wannan dai shi ne karon farko da ake yin irin wannan taro a Turai kuma ana sa ran kwararrru fiye da 100 za su halarci taron wanda Australiya ta shirya bisa hadin gwiwar Indonesia.

Ana zargin cewa kudaden da 'yan ta'adda ke yin musaya a tsakaninsu sun ninka sau uku a kasar ta Australia a cikin shekara guda, musamman saboda masu tayar da kayar baya 'yan Australia da ke tafiya Syria Iraki domin yin yaki.

Masu halartar taron sun ce gano wuraren da 'yan ta'adda ke boye kudadensu yana da matukar wuya saboda sau da dama ana boye kudaden ne a asussan bankuna na halas.