Congo- An zargi sojoji da yi wa mata fyade

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Binciken da Majalisar Dinkin Duniya ta yi ya nuna cewa cin zarafin da sojojin Congo suka yi duk ya fi muni a wannan shekarar.

Wani bincike da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya ce sojojin Congo sun yi wa mata 14 fyade cikin kwana biyu.

Shugaban sashen kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya a kasar, ya ce wannan shi ne mafi muni cikin duk rahotannin ire-iren cin zarafin da dakarun sojin kasar suka aikata a wannan shekarar.

Wasu kauyukan ma sunyi korafin cewar sojojin na damun su da fashi da makami da kuma cin zali.

Kakakin gwamnatin bai tanka game da wannan zargi ba, amma ya ce gwamnatin kasar na iya kokarin ta domin ganin ta yaki duk wani cin zarafi ta hanyar yin lalata da mata a Congo, inda abin ya fi kamari.

Binciken da aka gudanar da farko ya nuna cewa cin zarafin ya faru ne lokacin da sojojin ke bata kashi da mayakan sa kai da ke kudancin yankin Kivu a gabashin kasar.

Ministan sadarwa na kasar ya shaidawa BBC cewa ana gudanar da bincike kan lamarin, kuma kasar ba zata lamunci hakan ba tunda babu wani gamsasshen bayani a kai, har sai shari'a ta yanke hukunci.