An kashe wasu 'yan sanda a Saudiyya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan sandan kasar Saudiyya sun bazama neman wadanda suka aikata wannan aika-aika

An harbe wasu 'yan sanda har lahira a kasar Saudiyya, lokacin da aka kai wa wata motar da suke ciki hari da safiyar ranar Laraba.

Ba a tabbatar ko su wanene suka kai harin da ya auku a gabashin yankin Qatif ba.

An dade ana samun tarzoma tsakanin jami'an tsaro da tsirarun musulmi mabiya darikar Shi'a da ke wannan yankin.

Al'umomin yankin sun sha korafin cewa an mayar da su saniyar ware, kuma a yanzu 'yan sanda sun bazama neman wasu da ake zargi na da alaka da wata zanga-zanga da aka yi a yankin a shekarar 2011.