Za a hana sanya Niqabi a Senegal

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Senegal ta ce za ta dauki matakin ne domin hana hare-haren 'yan ta'adda.

Ministan cikin gida na kasar Senegal ya ce kasarsa tana shirin haramta wa mata sanya niqabi a bainar jama'a a yunkurin da take yi na hana kai hare-haren 'yan ta'adda.

Abdoulaye Daouda ya kara da cewa bai kamata a kalli lamarin a matsayin "nuna kiyayya ga Musulmai ba", saboda Senegal kasa ce da Musulmai suka fi yawa.

Idan aka hana sanya niqabi a Senegal, za ta kasance kasa ta biyar da ta haramta sanya shi a Afirka.

A makon jiya Shugaba Macky Sall na kasar, wanda shi ma Musulmi ne, ya yi kira da a dauki kwararan matakai na yaki da 'yan ta'adda.