Me ya kamata ka yi a lokacin da aka kai hari?

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gidan rawa na Bataclan na daga cikin wuraren da aka kai hari a Faransa.

Ba a cika samun munanan hare-hare kamar irin wadanda aka kai birnin Paris ba, wadanda suka yi sanadiyar mutuwar mutane 129, tare da jikkata fiye da 400.

Hukumomi suna shiryawa irin wadannan al'amura na gaggawa, amma wacce shawara ya kamata a bai wa sauaran jama'a kuma?

Da yawa daga cikin wadanda suka tsira daga hare-haren Paris sun ce sun dauka harbe-harben bindigar da suka fara ji wasan wuta ne ake yi.

John Leach, wani mai bai wa wadanda suka tsira daga hare-hare da kuma sojojin da suka je fagen fama suka dawo da rai shawarwari, kan yadda ba za su bari abubuwan rudanin da suka gani a can ya dinga firgitasu ba, ya ce yawanci irin hakan na faruwa.

Mutanen da basu tsammaci harbe-harben ba za su zaci wani abun ne daban, saboda sam basa kawo hakan a ransu. Ya ce, "Muna yawan yadda da abin da muke tunani ne ba mu cika yadda da abin da yake faruwa a zahiri ba, shi yasa muke yawan samun kanmu cikin hadari.

"Yi abin da ya kamata da hanzari"

Tsayawa tunanin me yake faruwa zai iya sawa ka samu kanka cikin wadanda suka sheka barzahu. Amma idan har mutum dama ya kan yi tunani hakan fa na iya faruwa a ko yaushe, to zai iya gaggawar sanin me ya kamata ya yi.

Mista Leach ya yi bayani cewa, "Abin da kawai ka ke bukata shi ne ka tambayi kanka ko akwai abin da ke faruwa ne, me zan fara tunani idan na ji abu makamancin haka?"

Yana da matukar sauki ka zauna a kantin cin abinci ko silima ba tare da mayar da hankali kan hanyoyi tserewa cikin gaggawa idan wani abu ya taso ba. Amma kuma sanin inda suke din na iya zama hanyar tsira.

A harin da aka kai gidan rawa na Bataclan a Faransa a Juma'ar da ta gabata, wani mai gadin wajen ya jagoranci mutane da dama ta wajen nuna musu hanyar fita ta gaggawa a wani sako na daban.

Mista Leach ya ci gaba da cewa mafi yawan mutane su kan rikice su kasa yin komai a lokacin da aka kai hari. Ya yi duba kan yanayin da ke barazana ga rayuwar mutane a duniya, inda ya gano cewa kashi 15 cikin 100 ne kacal suke yadda da abin da ke faruwa ta yadda har hakan kan taimake su su tsira. Kashi 75 cikin 100 kuwa basa kawo wa ransu cewa wani abu mara kyau zai faru a kusa da su kwatra-kwata. Sauran kashi goma cikin 100 kuwa suna rugar tsakani ne.

Idan aka kai hari a waje mai matsi ko rufaffe, to harsashi daya na iya ji wa mutane da dama rauni. Buya kuwa na rage hadarin samun kanka cikin wadanda harsashin zai samu sannan kana iya tsira daga wutar da wajen zai iya kamawa.

"Mai rabon ganin badi"

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu da suka samu tsira daga hare-haren Faransa.

Wadanda suka tsira da dama a Paris sun yi hakan, ta inda suka dinga buya a karkashin tebura ko bayan dirma-dirman sifukun rediyo. Amma rashin maboya a kan dandaryar kasan wajen ya sa ba kowa ne ya samu zarafin buya ba.

Wasu ma'aurata 'yan kasar Ireland kuwa, sun tsira saboda sun yi lambo tamkar matattu a lokacin da ake harbe-harben.

Wata wacce itama ta tsira Theresa Cede, ta shaida wa BBC cewa, "Wani saurayi ya ji mummunan rauni don haka ya nata kara, sai muka ce masa yi shiru ka nutsu kuma ka daina motsi, saboda a duk lokacin da aka yi motsi a wani sashe sai ka ji an yi harbi ta wajen. Suna neman ta inda ake motsi ne don kai hari wajen."

Wasu mutanen a Bataclan basu nemi hanyar tsira ta gaggawa ba a lokacin da maharan suka dan tsahirta. Duk da cewa yin hakan na da hadari amma kuma wasu na samun tsira ta yin hakan.

A ta bakin wadanda suka shaida lamarin hare-haren na ranar Juma'a da idonsu, mutane da dama sun zabi su buya a ofisoshi da ban daki har sai an kawo musu agaji.

"Fito-na-fito"

Hakkin mallakar hoto
Image caption Jami'an tsaron Faransa sun kawo taimakon gaggawa bayan kai harin.

Duk da cewa akwai hadari, amma wasu na ganin zai fi muhimmanci a yi fito-na-fito da maharan idan ta kama.

Wani kwararre a kan maslahar yin garkuwa da mutane James Alvarez, ya ce mayakan IS ba su cika yin garkuwa da mutane ba. Ya kara da cewa "Ba bu wanda ma za a sasanta da shi, su a wajensu kimarka ita ce su ganka a mace. Idan dai har na san cewa zan mutu to ba fa zan bayar da wuya cikin sauki ba ni ma."