An fara rijistar 'yan gudun hijira a Abuja

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan gudun hijira a Najeriya

Hukumomi a Najeriya sun fara yi wa 'yan gudun hijira da ke zaune a birnin tarayya Abuja rijista domin sanin adadinsu.

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasar-NEMA, da kuma hukumar kare hakkin dan'adam a aksar ne suke gudanar da rijistar.

Wata jami'ar NEMA, Chinwe Okpara ta ce bayaga sanin adadin 'yan gudun hijirar, rijistar wadda ke gudana a cibiyoyi bakwai, za ta bai wa hukumar damar tallafa musu.

Jami'ar ta ce hukumar ba za ta dauke 'yan gudun hijirar ba daga inda suke ba, amma an basu damar yin zaban inda suke so su ci gaba da zama, ko a Abuja ko kuma garuruwansu.

'Yan gudun hijira sun fito ne daga wasu garuruwan jihar Borno musamman Gwoza da Bama.

A cewar hukumomi, wannan mataki zai taimaka wajen kyautata rayuwarsu ta hanyar sama musu matsuguni, da ilmantar da 'ya'yansu.