'Boko Haram ta kusa zuwa karshe'

Image caption Boko Haram na kara zafafa kai hare-hare

Masu sharhi kan al'amuran tsaro a Najeriya sun ce karshen Boko Haram ya zo a shi ya sa 'yan kungiyar ke kai hare-haren kunar-bakin-wake.

Hussaini Munguno, wani masanin sha'anin tsaro ya ce 'yan ta'adda ba sa nuna gazawarsu ko da kuwa a zahiri sun galabaita.

Ya kara da cewa sojojin Najeriya sun karya lagon kungiyar sannan sun tarwatsa su.

Monguno ya ce cikin kankanin lokaci kungiyar za ta zama tarihi.

Sai dai kuma wannan sharhin yana zuwa ne a dai-dai lokacin da wani sabon rahoto da aka fitar ya bayyana kungiyar ta Boko Haram da wadda ta zarta kungiyar masu da'awar jihadi ta IS a matsayin kungiyar ta'addanci mafi muni a duniya.