Wayoyin masu wuyar sha'ani kan tsaro

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wayoyin dai suna da wuyar sha'ani ta fannin tsaro

Ofishin mai shari'a na lardin Manhattan da ke Amurka ya ce ya kamata jami'an tsaro su samu damar samun boyayyun bayanai daga wayoyin zamani na komai-da-ruwanka ko kuma smartphones.

Ofishin ya nuna shakku kan manufar Apple da Google wadanda tsarin wayoyinsu na iOS da Android suke boye bayanai.

Ya kara da cewa abun da kamfanonin guda biyu suke yi wajen boye bayanai yana da matukar illa a kan al'umma.

A baya-bayan nan dai kamfanin Apple ya ki amince wa da wani umarnin kotu na ya bude wata waya domin samun bayanai kan wani babban laifi da aka yi.

An ce an mika wa kamfanin jerin wasu laifuka da aka aikata da wayoyin kamfanin na smartphones, da manufar ya bude tsarin da ke boye bayanai domin gano masu laifin.

A baya dai ofishin mai shari'ar ya rubuta wasiku daban daban ga kamfanonin biyu domin neman karin bayani kan halayyar da suke nunawa ta kin bude wayoyin.

Sai dai kuma ofishin mai shari'ar ya ce har yanzu ba bu wanda ya mayar masa da martani.

Hakkin mallakar hoto GETTY IMAGES
Image caption Masu amfani da wayoyin suna iya boye bayanan da ba sa son a gani.

Yanzu haka mai shari'ar yana son a rinka aika wa da kamfanonin sammace da zai tilasta musu bude tsarin sirri da ke wayoyin nasu.