Rawar da ma'aikatan jinya ke takawa a filin yaki

Image caption Marie-Ange na taimakawa mutane da yawa.

A duk lokacin wani rikici ko yaki, a kan samu wata tawaga ta mata da ke gwagwarmaya domin ganin sun ceto rayuka. Wadannan sojoji su ne ma'aikatan jinya, ko nas-nas.

A ci gaba da jerin shirye-shiryenmu na musamman na Mata 100: Muryar Rabin Al'ummar Duniya, mun duba wannan aiki da ma'aikatan jinya ke yi.

A Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, kasar da yaki ya daidaita, wata nas tana aiki don ceto iyalai -- amma ba daga bama-bamai ko harsasai ba. Fafutukar da take yi, ita ce ta ceto mutane daga mummunan tasirin rashin tsaro, da tamowa, da zazzabin cizon.

"Suna na Marie Ange Koutou. Ni nas ce a asibitin Kabo.

Iyalanmu ne ke shan wahala, shi ya sa na zabi yin wannan aikin, don na taimaka wa iyalan da ba su da lafiya.

A shekaru ukun da suka wuce an ga tashe-tashen hankula mafi muni a kasar, inda maykan sa-kai dauke da makamai suke ci karensu ba babbaka a yankunan karkara.

Yaran da ke nan suna da matsala saboda ba abin da iyayensu ke yi. Suna fama da matsala wajen tufatar da kawunansu, da zuwa makaranta, da ma cin abinci saboda ba damar yin noma.

Dalili shi ne idan suka fita suka tafi gona za a iya kashe su. Gungun matasa kan harbi shanunsu har ma da mutane. Don haka mutane ke tsoron zuwa gona.

Ta sadaukar da abubuwa da dama a rayuwarta don ta yi aiki a wannan wuri, inda take rayuwa daruruwan kilomita nesa da iyalinta.

Ina da 'ya'ya hudu.

Tun Kirsimetin bara, Marie-Ange ba ta ga 'ya'yanta ba.

Abu ne mai wahala, saboda kamata ya yi a ce yaran suna tare da ni. Amma saboda matsalar tsaro ba zan iya kawo su nan ba.

A nan tamkar bakuwa ce ni saboda babu wani dan uwana.

Saboda matsalar tsaro, idan mutum bai yi taka-tsantsan da abin da zai fada ba sai wani ya kai masa hari.

Shi ya sa da zarar na tashi daga aiki sai na nufo gida kai-tsaye. Idan akwai wasu 'yan abubuwa da zan yi sai na yi, idan ba haka ba sai na dawo gida na kwanta.

Ranar Lahadi na kan ce coci, na kuma dawo salun alun.

Ina fata nan gaba da taimakon Allah abubuwa za su inganta. Ina fatan Allah Ya sa a samu wani yanayi da 'ya'yana za su rayu a kasar nan cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali".