Burundi ta ce 'yan Belgium su bar kasar

Hakkin mallakar hoto
Image caption Dangantaka tsakanin Burundi da Belgium ta sukurkuce

Jam'iyyar da ke mulki a kasar Burundi ta gargadi dukkanin 'yan kasar Belgium da ke zaune a kasar da su tattara inasu- inasu su bar kasar.

Jam'iyyar ta fitar da wannan sanarwa ce wasu 'yan kwanaki bayan da Belgium din- wacce a baya ta yi wa Burundin mulkin mallaka-- ta shawarci 'yan kasarta da su bar Burundin saboda karuwar tashe- tashen hankulan da ke faruwa.

An kashe mutane fiye da 200 tun daga watan Afrilu, lokacin da Shugaba Pierr Nkurunziza ya sanar da cewa zai tsaya takarar shugaban kasa a wa'adin mulki na uku.

Kuma a watan Yulin da ya gabata ne ya lashe zaben.

Burundi ta zargi Belgium da alaka da kungiyoyin 'yan adawa, da tace sune keda alhakin kashe- kashen da ake ta yi a cikin kasar