Kai tsaye: Harin da aka kai a Mali

Latsa nan domin ka sabunta shafin:

Hakkin mallakar hoto AP

Hukumomi a kasar Mali sun ce a yanzu an kawo karshen garkuwa da mutane da wasu 'yan bindiga suka yi.

'Yan sandan kasar Mali sun kutsa kai cikin otal din Radisson Blu, inda 'yan bindiga suka yi garkuwa da fiye da mutane 170.

Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP, ya ambato wani minista na cewa 'yan bindigar sun kashe mutane uku.

Ministan ya ce jami'an tsaro sun ceto kusan mutane goma.

A sanarwar da otal din ya fitar, ya ce mutane biyu sun rufe baki 140 da ma'aikatan otal din 30 "a wani daki a yanayi irin na yin garkuwa" da mutane.

'Yan kasashen waje da ke aiki a Mali ne suka fi zama a otal din, mai dakuna 190.

8:35 Nan muka kawo karshen labaran abinda ya faru a Mali kai tsaye.

Majalissar dinkin duniya ta ce mutane a kalla 27 ne suka mutu a harin da aka a otal din Radisson Blu dake Bamako a Mali.

Sai dai babu tambaci idan ko jami'an tsaro sun kammala aikinsu na dawo da doka da oda a otal din da kewayensa, amma dai babu wasu sauran mutane da ake garkuwa da su.

Bari mu barku da hoton dunbin jama'ar kasar Mali da suka taru suna jinjinawa jami'an Mali bisa yadda suka gudanar da aikinsu.

Hakkin mallakar hoto Reuters

8:28 Babu dan kasar Faransa da aka kashe a harin da aka kai Mali

Ministan Tsaro na kasar Faransa ya sanar da kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa babu wani dan kasar Faransa da aka kashe a harin da aka kai wa otal din Mali.

8:06 A wata sanarwa ta kafar sada zumunta ta Twitter shugaban kasar Mali, Ibrahim Boubacar Keïta zai yi taron gaggawa da Ministocinsa a Bamako a dai-dai wannan lokacin.

8:04 An kashe 'yan bindiga biyu da mutane 27 da aka yi garkuwa da su a otal din Radisson Blu a wani rahoto da majalissar dinkin duniya ta fitar in ji kamfanin dillacin labarai na Associated Press.

8:00 Wani dan jarida dan kasar Faransa, François Rihouay ya shaida wa BBC cewar da akwai tambayar da ake bukatar amsa cewa ta ina 'yan bundigar suka samu motai mai lambar diplomasiyya suka shiga otal din?

Wani ma'aikacin otal din mai aikin kula da ciyayi ya ce yaga maharan da idanunsa a lokacin da suka shiga otal din a bakar mota mai dauke da lamabar diplomasiyya.

Kuma maharan sun rufe fuskokinsu, tun daga bakin kofar otal din jami'an tsaro suka tsaida su, amma sai suka maida martani da yin harbe-harbe in ji wanda ya shaida lamarin.

730 Ministan tsaro na kasar Mali ya shaida wa Reuters cewa 'yan bindigar suna nan a cikin otal din da suka kai wa hari tun da safiyar yau.

"'Yan bindigar ba sauran mutanen da suka yi garkuwa da su a hannunsu, kuma jami'an tsaron Mali na kokarin damke su, in ji mai magana da yawun gwamnati Amadou Sangho.

7:23 Shin mahara nawa ne suka kai wa otal din Radisson Blu na Bamako hari ne?

Thomas Fessy da yake aika rahoto daga wajen otal din Radisson Blue ya ce "Awa bakwai aka dauka daga fara arangama da maharan har zuwa lokacin da jami'an tsaro suka kubutar da mutane daga otal din, kuma a yanzu an killace wurin da abin ya faru"

Wasu na cewa sun kai daga mutane biyu zuwa dozin daya, amma babu wanda ya tantance yawansu.

Jami'an tsaro suna raka wadanda aka kubutar daga otal din

Hakkin mallakar hoto bbc

7:12 Wa yake da alhakin harin da aka kai a Mali?

Al-Qaida da al-Murabitoun sun ce sune ke da alhakin harin da aka kai otal din Radisson Blu in ji kafar yada labarai ta Al-Akhbar.

Al-Akbar ita ce kafar yada labarai da al-Murabitoun wacce Mokhtar Belmokhtar ke jagoranta ke amfani da ita wajen isar da sakwonninta.

7:05 Ko za a iya danganta harin Mali da wanda aka kai kwanaki bakwai a Faransa?

Brett McGurk mataimaki na musamman ga tawagar shugaban Amurka ya sanarwa da kafa yada labarai ta MSNBC cewa ya yi wuri a tantance dangantakar hare-haren biyu.

7:00 Ga hotunan wadanda aka kubutar daga otal din suna kokarin fita daga otal din

6:51 Ga jumullar wadanda ake cewar sun tsira daga maharan

 • Mutane bakwai 'yan kasar Algeria in ji kamfanin dillacin labarai AFP
 • Mutane shida 'yan kasar Amurka in ji kamfanin dillacin labarai na AP
 • Mutane biyar 'yan kasar ma'aikatan kamfanin jirgin sama na Turkiya in ji kamfanin dillacin labarai na AP
 • Ma'aikatan kamfanin jirgin saman Faransa su 12
 • 'Yan kasar Raha biyu R
 • Dan kasar Ivory Coast in ji kamfanin dillacin labarai na AP
 • Ma'aikatan gidan talabijin na China hudu
 • Da kuma 'yan kasar India su 20 da suke daf da ginin da aka yi garkuwa da mutanen.

6:37 Ministan tsaro na kasar Mali, Salif Traore, ya sanar a wani taro da 'yan jaridu cewar babu wani mutun da yanzu haka ke hannun 'yan bindigar da suka yi garkuwa a otal din Radisson.

Shugaban kasar Mali ya yi godiya ta kafar sada zumunta ta twitter ga dukkan wadanda suka bayar da gudunmawa aka kawo karshin harin da aka kai-wa otal din.

Hakkin mallakar hoto AFP

6:25 Rahotanni na cewa Al-Mourabitoun ta ce ita ce ke da alhakin kai hari a otal din Radisson Blu dake Bamako a Mali, babu wanda ya tantance rahoton, amma dai Al-Mourabitoun tana da karfi a Arewacin Afirka wacce dan kasar Algeria Mokhtar Belmokhtar yake shugabanta.

4:14 Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ambato wata kungiyar masu jihadi mai suna al-Murabitoun tana cewa ita ta kai hari a otal din Radisson Blu da ke Bamako.

Kungiyar ta fitar da sanarwar ce a shafinta na Twitter, sai dai Reuters bai tabbatar ko shafin nakungiyar ne ba.

4:04 Karin bayani kan 'yan kasashen da ake garkuwa da su:

 • Mutane 30 ma'aikatan otal din ne
 • Mutane 20 'yan kasar India
 • Mutane 10 'yan China
 • Mutane bakwai 'yan Algeria
 • Mutane shida ma'aikatan diplomasiyya
 • Mutane shida ma'aikatan kamfanin jirgin saman Turkiyya
 • Mutane biyu 'yan kasar Morocco
 • Mutane biyu 'yan kasar Rasha da ke aiki da ke aiki da kamfanin jirgin saman Ulyanovsk
 • Mawakin kasar Guinea Sekouba Bambino yana cikinsu
 • Wasu 'yan kasar Faransa, cikinsu har da ma'aikatan kamfanin jirgin saman Air France 12
 • Amurkawa

3:50 Wani jami'in kasar Amurka ya shaida wa BBC cewa sojin Amurka 25 na cikin birnin Bamako domin taimakawa wajen ceto wadanda harin ya rutsa da su.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jami'an tsaro sun kubutar da mutane da dama.

3:16 Ma'aikatar tsaron Mali ta ce an kashe uku daga cikin 'yan bindigar da suka kai hari a otal din Radisson da ke Bamako, a cewar wani shafin intanet na Mali Abamako.