Mali: 'Yan sanda sun kutsa kai cikin otal

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan sanda sun yi wa otal din kawanya.

'Yan sandan kasar Mali sun kutsa kai cikin otal din Radisson Blu, inda 'yan bindiga suka yi garkuwa da fiye da mutane 170.

Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP, ya ambato wani minista na cewa 'yan bindigar sun kashe mutane uku.

Ministan ya ce jami'an tsaro sun ceto kusan mutane goma.

A sanarwar da otal din ya fitar, ya ce mutane biyu sun rufe baki 140 da ma'aikatan otal din 30 "a wani daki a yanayi irin na yin garkuwa" da mutane.

Wasu jami'an tsaro sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa 'yan sanda sun yi wa otal din kawanya.

'Yan kasashen waje da ke aiki a Mali ne suka fi zama a otal din, mai dakuna 190.

Wani dan kasar China ya gaya wa kamfanin dillancin labaran kasar na Xinhua ta hanyar manhajar wayar salula cewa yana cikin 'yan China da dama da lamarin ya rutsa da su.

A watan Agusta, wadansu 'yan bindiga da ake zargi masu kaifin ra'ayin addini ne sun kashe mutane 13, cikinsu har da ma'aikatan majalisar dinkin duniya guda biyar, lokacin da suka kai hari wani Otal a garin Sevare.