Mali: An ceto mutanen da aka yi garkuwa da su

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jami'ai na musamman sun kutsa ciki otel din Radisson Blu, inda suka ceto mutanen da 'yan ta'addan ke garkuwa da su.

Jami'ai a kasar Mali sun ce an gama ceto mutanen da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a wani otel da ke Bamako, babban birnin kasar.

Jami'an tsaro na musamman sun kutsa kai cikin otel din mai suna Radisson Blu, bayan maharan sun shiga da harbe-harbe suna kabbara, inda suka tsare mutane 170.

Otel din dai mallakin Amurkawa ne, kuma yana da farin jini a wajen baki 'yan kasashen waje da ke sauka a cikinsa.

Jami'ai sun ce mutane a kalla 18 ne suka mutu, yayin da sojoji biyu suka samu rauni.

Cikin wadanda aka kashe har da wani dan majalisar dokokin kasar Belgium, Geoffry Dieudonne da ya fito daga yankin Wallonia.

Amurka da Faransa sun aika jami'an tsaro na musamman domin taimakawa wajen ceto mutanen.

Wannan hari na zuwa kwanaki kadan bayan harin da aka kai a birnin Paris, duk da cewar babu wata alama da ke nuna cewa akwai alaka tsakanin su.