Kalubalen da matan karkara a Nijar ke fuskanta

Image caption Matan karkara na kwashe tsawon lokaci kafin su samu ruwan sha.

Matan karkara a nahiyar Afirka na fuskantar kalubale da dama wajen kula da iyalinsu.

A ci gaba da shirinmu na Mata 100: Muryar Rabin Al'ummar Duniya, wata mata a Jamhuriyar Nijar mai suna Nana Sailuba, ta shaida wa BBC cewa tunda sanyin safiya take fara ayyukan gidanta.

A cewar ta, "Idan gari ya waye ina zuwa rijiya, sannan na je na saro itace, kana na dawo gida na yi surfe da neman ruwan ban-ruwa".

Sailuba, 'yar kimanin shekaru 25 da haihuwa, wacce ke zaune a garin Tsauni na jahar Damagaram, ta kara da cewa, "ina yi wa yara abinci da hada musu fura, sannan na yi musu wanka da wanki. Daga nan sai na tura su makaranta".

Ta ce babu abin da yake burge ta a rayuwar duniyar nan kamar tafiya kasar Algeria domin neman kudi, tana mai karawa da cewa amma an koro ta.