An yi garkuwa da mutane 20 a Afghanistan

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mayakan Sunni a Afghanistan

Kimanin mambobin kabilar Hazara 'yan tsirari ashirin aka sace a kudancin gundumar Zabul Afghanistan.

'Yan bindigar wadanda har yanzu ba a kai ga gane ko suwaye ba, sun yi garkuwa da mutanen ne bayan sun tsayar da motoci kirar bas-bas din da suke ciki a kan wata babbar hanya.

Kimanin shekara guda ke nan da mayakan sunnin su ka yi garkuwa da mutanen Hazara wadanda 'yan shi'a ne, kuma sun yin hakan ne domin tursasawa gwamnatin Afghanistan ta sako 'yan uwansu da ke zaman gidan kaso.

A wancan lokacin an sako wasu 'yan kabilar Hazaran, wasu kuma sun kashe su ciki har da wata mata da wasu yara mata biyu wadanda aka yanka su a farkon watan da muke ciki.