Babu dalilin kai samame gidana — Bafarawa

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Attahiru Bafarawa na da kusanci da tsohon mai bai wa Shugaban Kasa shawara kan sha'anin tsaro, Kanar Sambo Dasuki

A Najeriya Tsohon Gwamnan Jihar Sokkoto kuma jigo a jam'iyyar adawa ta PDP Alhaji Attahiru Bafarawa ya bayyana cewa babu dalilin da zai sa hukumar EFCC ta kai samame gidansa, ya na mai zargin cewa samamen wani yunkuri ne na bata masa suna .

Attahiru Bafarawa ya ce a iya saninsa babu wata gayyata da hukumar ta EFCC ta yi masa da ya ki amsawa da zai sa jami'anta su yi wa gidansa dirar mikiya.

A ranar Alhamis ne dai jami'an hukumar EFCCn su ka yiwa gidan Alhaji Attahiru Bafarawan dirar mikiya, sai dai tsohon gwamnan ba ya Nigeriar a lokacin.

A baya dai hukumar EFCC ta zargi Alhaji Bafarawa da wasu mutane 15, mafiyawanci masu taimaka masa a lokacin da ya ke gwamna, da yin wadaka da kudaden al'umma da suka tasamma N15 billiyon.