Minista a Kenya ta yi murabus

Hakkin mallakar hoto WAIGURU TWITTER
Image caption Anne Waiguru

Wata minista a Kenya ta yi murabus bayan zarge-zargen cin hanci da rashawa da a ka yi mata.

Anne Waiguru ta ce ta yi hakan ne domin ta bi ka'idojin da likita ya shimfida mata da kuma shawarwari bayan abin da ya faru a ma'aikatar ta wanda ta kai har lamarin ya shafi lafiyarta da kuma iyalanta.

Ana zarginta da abinda ta kira bita da kulli wanda wasu 'yan siyasa ko kuma jam'iyyu ke yi wajen juya akalar yaki da cin hanci da rashawa a kanta.

A farkon watan nan, Ms Waiguru ta bayyana gaban wani kwamitin majalisar dokokin kasar.

An tambayeta a kan jerin zarge-zargen rashin bin doka da ka'ida da kuma sayen abubuwa masu tsada ga ma'aikatarta ciki har da wata talbijin da a ka saya a kan kudi dala dubu 19.

Wasu 'yan majalisar dokokin daga jam'iyya mai mulki sun yi kira da a tsige ta in da suke cewa ta na kawowa shugaban kasar cikas a aiki.

Ms Waiguru ta nisanta kanta daga duk wasu zarge-zargen cin hanci inda ta ce bata sayi wani abu domin ma'aikatar ta ba.

Ta ce wadannan zarge-zargen sun fara ne tun lokacin da ta yi yunkurin tona asirin wasu jami'ai da suka saci kudi daga asusun hukumar kula da matasa wadda ta na karkashin ikonta.