Mali na farautar wasu mutane game da hari

Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keit Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keit

Jami'an tsaron Mali sun ce suna farautar a kalla mutane uku wadanda suke zargi bayan harin da yan bindiga suka kai wani babban Otel a Bamako babban birnin kasar.

A halin da ake ciki gwamnatin kasar ta ayyana dokar ta baci na kwanaki goma da kuma zaman makoki na kwanaki uku

Mutane 19 suka rasu wadanda suka hada da Rashawa shidda da yan China uku da kuma wani Ba Amurke daya.

An kashe 'yan bindiga biyu lokacin da sojoji suka afka otel din domin ceto mutane fiye da 130 da yan bindigar suka yi garkuwa da su.

Shugaban kasar China Xi Jinping ya yi Allah wadai da harin ya kuma yi alkawarin bada karin hadin kai domin yaki da ta'addanci.