MDD ta amince kasashen duniya su yaki IS

Image caption Taron kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya

Kwamitin tsaro na majalisar Dinkin Duniya ya amince da wani kuduri, da ya bukaci duk kan kasashen da ke da iko, da su shiga a dama da su a yaki da kungiyar IS.

Kudurin ya yi kira ga kasashen mambobin Majalisar Dinkin Duniyan da su lalata tungar kungiyar IS a Syria da Iraki.

Kazalika, kudurin ya bukaci a rubanya fafutukar da ake yi, tare da amfani da duk kan matakin daya zamo wajibi domin ganin bayan kungiyar ta IS.

Faransa ce ta gabatar da daftarin kudurin bayan hare haren da aka kaddamar a Paris, inda ta bayyana kungiyar IS a matsayin wata babbar barazana ga zaman lafiya da tsaro a duniya.

Faransar ta ce tuni hujjoji suka bayyana na amfani da karfin soji a kan kungiyar, saboda 'yan cin da kasashe suke da shi na su kare kansu.