Belgium—Ana neman Salah Abdeslam ruwa a jallo

Hakkin mallakar hoto Press Association

Tashoshin jiragen kasa a birnin Brussels na Belgium zasu ci gaba da kasancewa a rufe akalla zuwa wani lokaci na yau Lahadi, har sai hukumomi sun sake nazarin halinda ake ciki dangane da tsaro.

An dai rufe su ne bayan da gwamnati ta daga matsayin ankararwarta na yiwuwar kai wani hari zuwa matakin kololuwa a ranar Jumu'ah, bayan hare- haren da aka kai a birnin Paris.

Shaguna da kuma gidajen kallo da dama sun kukkulle kofofinsu a jiya asabar, sannan an soke gudanar da bukukuwa.

An yi imanin cewa daya daga cikin wadanda suka kai hari Paris Salah Abdesslaam ya tsere ne zuwa kasar ta Belgium

Kuma har yanzu ana ci gaba da farautar sa, bayan da aka bayyana shi a matsayin mutumin da ake fi nema ruwa a jallo a nahiyar Turai.