Ba a sanar da wanda ya lashe zaben Kogi ba

Masu kada kuri'a a Najeriya
Image caption Mutane dai na zuba ido su ga jam'iyyar da za ta lashe zaben tsakanin PDP da APC.

A Najeriya, hukumar zabe mai zaman kan ta INEC ta ce har yanzu sakamakon zaben gwamna da aka gudanar a jihar Kogi dake shiyyar arewa ta tsakiya bai kammalu ba.

Hukumar ta ce sai an sake zaben karo na biyu, sannan za a sanar da wanda ya yi nasarar darewa kujerar gwamnan jihar, tsakanin Idris Wada na jam'iyyar PDP, da Prince Audu na jam'iyyar APC.

A ranar Asabar ne al'ummar jihar suka kada kuri'unsu don zabar gwaninsu a zaben da ake gani mai zafi musanman tsakanin jam'iyyar mai mulki a jihar PDP da kuma APC.

Rahotanni sun ce an samu 'yan matsaloli a wasu wurare a lokacin zaben wajen amfani da na'urar tantance masu zabe.

Kimanin jami'an 'yan sanda dubu 15 aka girke a lokacin zaben, da kuma gabanin sanar da sakamakon zabe.