Mutane biyu sun mutu a zanga-zangar Nepal

Masu zanga-zanga a Nepal
Image caption Masu boren na adawa da sabon kundin tsarin mulkin kasar.

'Yan sanda a kudu maso yammacin Neoal, sun tarwatsa masu zanga-zangar kin amincewa da sabon kundin tsarin mulkin kasar, tare da hallaka mutane biyu.

Jagoran masu boren ya ce an hallaka mutanen ne a lokacxin da suke zaune a gefen wata babbar hanya da su ke gyra cunkoson ababen hawa.

Su kuma jami'an tsaron sun ce masu zanga-zangar su na jifan 'yan sanda da duwatsu da bam din da aka hada shi da fetur.

Fiye da mutane arba'in ne suka rasa rayukansu, tun bayan sanar da sabon kundin tsarin mulkin kasar a watan Satumbar da ya wuce, yawancin su 'yan kabilar Madhesi ne da suke da shigen al'adu daya da India.

Inda sukai ikirarin cewar sam babu ta inda za su samu tagomashin gwamnatin kasar a sabon kundin tsarin mulkin.

Ya yin da gwamnatin Nepal ke zargin kasar India da marawa 'yan kabilar ta Madhesi baya a boren da suke yi.

A bangare guda kuma likitoci a babban birnin kasar Kathmandu, sun ce rufe hanyoyin da masu boren suka yi ya sanya yawancin asibitoci rasa magunguna da sauran abubuwan bukatu.