Dan takarar gwamna na APC a Kogi ya rasu

Image caption Marigayi Prince Abubakar Audu, dan takarar jam'iyyar APC a zaben gwamnar jihar Kogi wanda ya rasu

Dan takarar gwamnan jihar Kogi a karkashin inuwar jam'iyyar APC Alhaji Abubakar Audu ya rasu.

Abubakar Audu ya rasu ne yau Lahadi sakamakon rashin lafiyar da ba a fayyace ba.

Wani makusancinsa ya tabbatarwa da BBC rasuwar ta Abubakar Audu.

A yau ne dai hukumar zabe a Najeriyar INEC ta baiyana cewa zaben gwamnan da aka gudanar a jihar a jiya Asabar bai kammala ba.