Qatar:Lauyan gwamnati zai daukaka kara

Hakkin mallakar hoto Getty

Babban lauyan gwamnatin Qatar zai daukaka kara a kan hukuncin kotu da ta wanke mutane da dama da suka hada da wani babban jami'in diplomasiyya a game da wata gobara da ta hallaka mutane 19 ciki har da yara 13.

A watan da ya wuce ne kotun daukaka kara ta sauya hukuncin kisa ba da gangan ba da ake tuhumar mutanen game da gobarar da ta tashi a wani wurin wasan yara da ke wani babban rukunin kantuna a Doha shekaru uku da rabi da suka wuce.

Daga cikin mutanen da kotun ta wanke har da Sheikh Ali bin Jassim al-Thani, jakadan Qatar a Belgium wanda yana daya daga cikin wadanda suka mallaki wurin wasan yaran.