Macri ya lashe zaben shugaban Argentina

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mauricio Macri ya zama shugaban Argentina

A kasar Argentina, magajin garin Buenos Aires, Mista Mauricio Macri ya zama sabon shugaban kasar.

Mista Macri shi ne dan takarar jam'iyyar hamayya da ke ra'ayin gargajiya.

Mista Macri ya lashe zagaye na biyu na zaben wanda shi ne karo na farko da zaben shugaban kasa a Argentina ya kai ga zagaye na biyu.

A zagayen farko na zaben cikin watan jiya, Mista Macri ya kasance yana bin abokin hamayyarsa a baya, wanda kuma tsohon mataimakin shugaban kasar ne, Daniel Scioli.

Wannan ya kawo karshen shekaru 12 da jam'iyyar 'yan gurguzu ta yi tana mulki a kasar karkashin jagorancin Cristina Fernandez de Kirchner, wadda kafin ita, mijinta mariganyi Nesto Kirchner ne shugaban kasar.

Tuni abokin hamayyar sa Daniel Siyoli ya amsa shan kaye a zaben.