Amurka ba abar yarda ba ce — Khamenei

Hakkin mallakar hoto press tv
Image caption Ali Khamenei ya ce Amurka da takwarorrinta ne ke daukar nauyin ta'addanci.

Babban jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya ce bai kamata a yarda da kasashen da ke ikirarin yaki da ta'addanci ba, yana mai zargin su da daukar nauyin 'yan ta'adda.

Ali Khamenei ya bayyana haka ne ranar Litinin a Tehran lokacin da yake ganawa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Shafin intanet na gidan talabijin din Press TV ya ambato Ali Khamenei yana cewa, "Gamayyar kasashen duniya da ke ikirarin yaki da 'yan ta'adda ba abin amincewa ba ne, saboda kasashen da ke rusa duniya irinsu Amurka ne ke kirkirar 'yan ta'dda irin su IS suke kuma taimaka musu."

Ali Khamenei ya kara da cewa "Makiyan Musulinci na fili da kuma wadanda ke ikirarin kare Musulinci amma suna tozarta shi, Danjuma ne da Danjummai."

Shugaba Buhari ya je Iran ne domin halartar taron kasashe masu albarkatun iskar gas na uku.