Kwararru sun soki WHO saboda ebola

Hakkin mallakar hoto Getty

Wani rahoto ya yi kakkausar suka ga irin martanin da kasashen duniya suka mayar a lokacin da cutar Ebola ta barke a yammacin Afirka-- wanda ya janyo mutuwar mutane fiye da dubu goma sha daya a kasashen Guinea, da Liberia da Saliyo.

Rahotan wanda wasu kwararru masu zaman kansu su ashirin suka fitar, ya yi kakkausar suka musamman akan irin rawar da hukumar lafiya ta duniya ta taka a lokacin da cutar ta barke

Rahotan ya yi kakkausar suka musamman akan hukumar lafiya ta duniya WHO, wanda yace saida ta dauki watanni Tara cur, kafin ta bayyana cutar a matsayin wata annoba

Do haka Kwararrun da suka wallafa rahotan suka ce wannan ya janyo kima da kuma girman hukumar ya ragu