INEC za ta yi nazarin doka kan rasuwar Audu

Image caption Nick Dazang ya ce hukumar zaben Najeriya tana sauraron APC

Sakamakon rasuwar dan takarar gwamna a jihar Kogi karkashin jam'iyyar APC, hukumar zaben Najeriya ta ce tana jiran jam'iyyar ta sanar da ita a hukumance kafin ta dauki mataki a kan lamarin.

Kakakin hukumar zaben Mista Nick Dzang ya shaida wa BBC cewa idan jam'iyyar APC ta sanar da INEC, za su duba tanadin da dokar zabe da kundin tsarin mulkin kasa da kuma kundin jam'yyar ta APC suka yi idan irin haka ta faru.

Mista Dazang ya ce hukumar zaben za ta dauki mataki ne kadai bayan jam'iyyar ta sanar da ita.

Tuni dai masana shari'a a kasar suka fara muhawara a kan al'amarin siyasar jihar Kogi, wanda suke cewa ba a taba cin karo da irin sa ba, inda dan takara ya rasu kafin a kammala zabe.

A ranar Lahadi ne aka sanar da rasuwar dan takarar gwamnan jihar Kogi a karkashin jam'iyyar APC a zaben da aka gudanar ranar Asabar, Alhaji Abubakar Audu.

Abubakar Audu ya rasu ne sakamakon rashin lafiyar da ba a fayyace ba.