Kogi: APC ta ce tana nazari kan dokokin Nigeria

Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta ce tana ci gaba da nazarin dokokin kasar domin sanin matakin da za ta dauka bayan rasuwar dan takarar gwamnan jihar Kogi a karkashin jam'iyyar, Alhaji Abubakar Audu.

Sanata Lawal Shuaibu, mataimakin shugaban jam'iyyar mai kula da shiyyar arewacin kasar, ya shaida wa BBC cewa lauyoyin jam'iyyar suna nazarin dokokin zaben kasar domin sanin inda za a dosa.

Ya ce a yanzu haka jam'iyyar tana jiran hukuncin da hukumar zaben kasar za ta yi.

Sai dai ya ce idan dai har hukuncin bai yi wa jam'iyyar dadi ba za ta kalubalanci hukumar zaben.

Sanata Shu'aibu ya kara da kore yiwuwar sake zabe a jihar domin, a cewarsa, jam'iyyarsu ta riga ta lashe zaben saboda haka sai dai idan za a sake zaben ne a tsakanin 'yan jam'iyyar ta APC.

A ranar Lahadi ne aka sanar da rasuwar dan takarar gwamnan jihar Kogi a karkashin jam'iyyar APC a zaben da aka gudanar ranar Asabar.

An kuma yi jana'izar sa ranar Litinin a garin Ogbonicha.

Abubakar Audu ya rasu ne sakamakon rashin lafiyar da ba a fayyace ba.