KOGI: APC za ta tsayar da sabon dan takara

Hakkin mallakar hoto Channels TV
Image caption Shugaban INEC Farfesa Mahmoud Yakubu

Hukumar zabe ta Najeriya INEC, ta bai wa jam'iyyar APC damar gabatar da sabon dan takarar gwamna a jihar Kogi da ke araewacin Najeriya, sakamakon mutuwar dan takarar jam'iyyar Abubakar Audu a ranar Lahadi.

Kazalika, INEC ta sanya ranar 5 ga watan Disamba ta zamo ranar da za a kammala zaben jihar a mazabu 91.

A ranar Asabar ne al'ummar jihar suka kada kuri'unsu don zabar gwaninsu a zaben da ake gani mai zafi musanman tsakanin jam'iyyar mai mulki a jihar PDP da kuma APC.

Daga bisani hukumar INEC ta ce zaben bai kammalu sai an sake a wasu mazabun.