Boko Haram: Ana jinkiri wajen tura sojoji filin yaki

Image caption Kanar Abubakar ya ce suna dab da murkushe Boko Haram.

Rundunar sojin Najeriya ta ce har yanzu akwai wasu kasashe da ba su bayar da dakarunsu domin shiga rundunar hadin gwiwa ta kasashen da ke makwabtaka da tafkin Chadi domin yaki da 'yan kungiyar Boko Haram ba.

A hirar da ya yi da BBC, Kakakin rundunar tsaron Najeriyar, Kanar Rabe Abubakar ya tabbatar cewa suna iya kokarinsu wajen murkushe 'yan kungiyar Boko Haram din kafin cikar wa'adin da aka dibar musu.

Ya ce wasu kasashe sun riga sun turo da nasu dakarun yayin da wasu na shirin turo da nasu.

Sai dai ya ce har yanzu bai san ranar da wadannan kasashe za su turo da sojojinsu ba.