Baraka ta kunno kai a jam'iyyar PDP

Hedkwatar jam'iyyar adawa ta PDP
Image caption Hedkwatar jam'iyyar adawa ta PDP

A Najeriya, ana ci gaba da cece kuce tsakanin 'ya'yan jam'iyar adawa ta PDP game da shugabancin jam'iyyar.

Wasu 'yan jam'iyyar daga arewa maso gabashin kasar sun garzaya kotu domin kalubalantar rashin mika wa wani dan jam'iyyar daga yankin jagorancinta, suna masu cewa hakan ya saba wa dokar jam'iyyar.

Wadanda suka shigar da kara -- karkashin jagorancin Barista Ahmed Gulak -- sun ce sun shigar da karar ne domin kotu ta fayyace musu kan ko jiga-jigan jam'iyyar suna da hurumin kin mika jagorancinta ga wani mutum da ba dan yankinsu ba ne ganin cewa shugaban da ya yi murabus bayan zaben kasar dan yankin ne.

A yanzu dai shugaban riko na jam'iyyar ba dan arewa maso gabashin kasar ba ne, kuma masu kalubalantar jam'iyyar na ganin bai kamata ya ci gaba da shugabancinta ba.

A makon da ya gabata ne dai, jam'iyar ta PDP ta gudanar da wani taro na kasa a Abuja, a wani mataki na dinke barakar da ke tsakanin 'ya'yanta tun bayan kayen da ta sha a babban zaben kasar.