Canada za ta rage yawan 'yan gudun hijira

'yan gudun hijira daga Syria Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan gudun hijira daga Syria

Gwamnatin kasar Canada ta ce za ta dauki 'yan cirani daga kasar Syria guda dubu goma kafin karshen shekaran nan, abin da ke nuna da ragi daga adadin da kasar ta yi alkawarin runguma tun farko.

Sai dai kuma gwamnatin ta ce tana kan bakanta na dibar karin 'yan hijrar dubu 15 daga nan zuwa karshen watan Fabrairun shekara mai kamawa.

A na dai ta faman sukar gwamnatin kasar kan cewa ta na yin gaggawa wajen kwasar masu gudun hijrar, sannan kuma hare-haren da aka kai birnin Paris ya kara sanya ta jan kafa wajen tantance masu kaurar.

Ministan kasar mai kula da shige da fice, John McCallum ya fadi cewa 'yan Canada ba za su so su yi gaggawa ba wajen aiwatar da shirin ba. Sannan kuma ya ce kasar za ta sanya ido wajen shigi da fici saboda gudun ta'addanci.