An haramta yi wa mata kaciya a Gambia

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yahya Jammeh ya ce muslinci bai yarda da yi wa mata kaciya ba.

Shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh ya haramta yi wa mata kaciya yana mai cewa ba al'ada ce da ake bukata a musulinci ba.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya ce mutane da dama sun barke da shewa bayan Yahya Jameh ya yi wannan sanarwa a lokacin wani gangami.

Hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin diniya ta ce an yi wa kashi uku bisa hudu na matan kasar kaciya.

A nau'in kaciyar da ya fi tsanani, bayan yanke dan-tsakansu, ana dinke kofar farjin mace ta yadda namiji ba zai iya saduwa da ita ba, ko kuma ba za ta ji dadin saduwar ba.

Kaciyar matan na da matukar zafi, kuma tana iya haddasa wa mace cutar sarke-hakora(tetanus) da cuta mai karya garkuwar jiki da ciwon hanta nau'oin B da C da hana haihuwa.