Kogi: APC na shirin yin zaben fitar da gwani

Marigayi Abubakar Audu
Image caption Marigayi Abubakar Audu

Jam'iyyar APC a Najeriya ta ce za ta yi zaben fitar da gwani na gwamnan jihar Kogi domin maye gurbin dan takararta marigayi Abubakar Audu.

Abubakar Audu ya rasu ne ranar Lahadi jim kadan bayan hukumar zaben kasar ta sanar da cewa ba a kammala zaben ba.

Matakin da jam'iyyar ta dauka ya zo ne bayan hukumar zaben ta bukace ta da ta mika wani dan takara a zaben gwamnan jihar da ta shirya kammalawa ranar biyar ga watan Disamba mai zuwa.

Hukumar zaben ta ce ta dauki matakin ne bayan da ta yi nazari a kan tanade-tanaden tsarin mulki da kuma dokokin zaben kasar.

Sai dai jam'iyyar hamayya, PDP ta soki matakin hukumar zaben na bai wa APC damar sake tsayar da dan takara, tana mai bukatar shugaban hukumar zaben da babban lauyan gwamnati da su sauka daga mukamansu.