Gwamnatin Nigeria za ta fara bai wa matasa N5000

Shugaba Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari

Gwamnatin Najeriya ta ce a shekara mai zuwa za ta soma aiwatar da tsarin bai wa matasa marasa aikin yi tallafin kudi na N5000 kamar yadda jam'iyyar APC mai mulki ta yi alakawari a lokacin yakin neman zabe.

Ministan matasa da wasanni Solomon Dalong shi ne ya bayyana haka a hirar da ya yi da BBC.

Mista Dalong ya ce tsarin ba ya cikin kasafin kudin bana, yana mai cewa hakan ne ya sa ba su fara aiwatar da shirin ba.

Sai dai ya ce gwamnati ta ware kudin da za ta kashe a karkashin wannan tsari a kasafin kudi badi.