Manufar ziyarar Paparoma zuwa Afrika

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mabiya darikar Katolika na murnar zuwan Paparoma Afrika

Paparoma Francis na ziyara a Afrika cikin wannan makon a karon farko, inda yayin ziyarar tasa zai je sansanin 'yan gudun hijira da yankunan da marasa galihu ke zama da kuma masallaci.

A yayin ziyarar tasa, wacce zai ke kasashen Kenya da Uganda da Jamhuriyar tsakiyar Afrika, zai gabatar da jawabai 19 a kan abubuwa kamar haka:

1. Zaman lafiya tsakanin Musulmai da Kiristoci

Ana sa rana zai fi mayar da hankali ne kan yadda za a dinga samun jituwa tsakanin mabiya addinai daban-daba, da zaman lafiya a irin wannan lokaci da rikice-rikice masu alaka da siyasa suka yawaita da kuma karuwar masu tsattsauran ra'ayin addini a nahiyar.

An tsaurara tsaro sosai a yayin wannan ziyara tasa, a lokacin da kiristoci suka yi dandazo domin ganin Paparoman, wanda a baya ya ce bai kamata Kiristoci su dinga yi wa Musulunci kallon addini mai son tayar da hankali ba.

Paparoma ya fara ziyarar tasa daga Kenya, kasar da ke fuskantar rikicin masu da'awar tsattsauran kisihin Islama. Shekaru biyu da suka gabata, wasu 'yan bindiga na kungiyar Al-Shabab suka hallaka a kalla mutane 67 cikin wani babban kantin kayan masarufi, a Nairobi babban birnin Kenya.

Daga Kenya Paparoman zai wuce Uganda, inda a can ma 'yan kungiyar Al-Shabab suka taba kai harin bam wajen kallon kwallo a Kampala, babban birnin kasar, inda mutane ke kallon wasan cin kofin duniya na shekarar 2010 a talbijin.

Kasashen Afrika biyar da suka fi yawan mabiya darikar Katolika

1. Jamhuriyar Dimokradiyar Congo: miliyan 31 2. Najeriya: miliyan 20 3. Tanzaniya: miliyan 14.2 4. Uganda: miliyan 14.1 5. Angola: miliyan 10.8

Bayanai daga ciyar addini ta Pew

Mutane da dama sun yi tunanin babban hatsari ne ya je kasa ta uku a jerin kasashen da zai ziyarta, wato Jamhuriyar tsakiyar Afrika, saboda dalilai na tsaro.

Amma wasu kuwa na ganin ziyarar Paproma zuwa Bangui, babban birnin kasar inda mutane da dama suka mutu sakamakon rikici tsakanin mayakan sa kai na Kirista "anti-balaka da kuma na Musulmai "seleka", ta dace kwarai a matsayinsa na shugaban addini.

A takaice ma suna ganin zai iya yin kira ga Kirista da Musulmai su zauna lafiya da juna.

2. Talauci

Image caption Ga dukkan alamau Paparoma zai yi jawabi ga talakawa

Ana ganin Paparoma a matsayin wani zakaran gwajin dafi wajen taimakon talakawa.

Yadda yake yawan nuna damuwa kan lamarin kasashe masu tasowa da kuma saukin kansa a cikin tasa rayuwar, zai zama abin maraba ga kasashen da karbar hanci da rashawa suka yi wa ka-ka-gida.

Haka kuma mutane na girmama shi wajen ganin yadda yake mayar da hankali kan al'amuran sauran kasashe ba wai na Turai ba kawai. Shi yasa ma ake ganin wannan Paparoma dai zai isar da sako ga mutanen da ake zalinta da wadanda ke cikin halin ka-ka-ni-ka-yi, wadanda ba ma mabiya addininsa ba kawai har ma na wasu addinan.

A Kenya, kashi daya na mutanen kasar ne suka mallaki kashi 75 cikin 100 na dukiyar kasar, don haka sakon Paparoma Francis zai yi farin jini sosai a wajen ragowar kashi 99 cikin 100 na al'ummar kasar.

Mai yiwuwa ya yi Allah-wa-dai da rashin daidaito da karbar hanci da rashawa, zai kuma ziyarci yankin marasa galihu da kabilun Kenya daban-daban kimanin 100,000 suke zaune.

3. Muhalli

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Paparoma ya ce sauyin yanayin duniya ya fi shafar mazauna kasashe masu tasowa

Mutane da dama za su mayar da hankali domin jin bayanin da Paparoma zai yi kan shirin raya muhalli na Majalisar Dinkin Duniya a Nairobi, dangane da tattaunawar da za a fara kan sauyin yanayin duniya a Paris, ranar 30 ga watan Nuwamba.

A wata makala da ya wallafa a farkon shekarar nan a kan muhalli, wacce ya aike wa da bishop-bishop, mai taken "Laudato Si," ya yi magana kan yadda al'umma ke mayar da doron kasa wata matattarar kazanta da shara. Akwai yiwuwar Paparoman zai fadi abin da ke zuciyarsa ba tare da noke-noke ba.

Ba shakka Paparoma zai jaddada bukatar da ke akwai ga kasashen duniya don dakatar da yadda ake mayar da doron kasa matattarar shara, wanda yake ganin talakawa ne hakan ya fi shafa.

A takaice, zai gayawa manyan masu arziki da su dinga la'akari da talakawa.

4. Luwadi da madigo

Hakkin mallakar hoto Isaac Kasamani l AFPl Getty
Image caption 'Yan luwadi na son Paparoma ya yi duba kan hakkokinsu

A Uganda kuwa, watakila 'yan luwadi da 'yan madigo ne ake tunanin za su yi kira ga Paparoman don ganin ya goyi bayansu wajen hana nuna adawa ga abin da suke yi a mafi yawan kasashen Afrika.

A can baya, da aka tambayi Paparoman a kan wani malamin coci dan luwadi, sai ya ce "Wane ne ni da zan yi alkalanci?"

Kazalika, taron majalisar coci da aka yi a Rome bai yi duba a kan ko cocin zai amince a karbi 'yan luwadi mabiya darikar katolika ba.

Shin ko akwai yiwuwar ya yi magana a kan wariyar da ake nuna wa 'yan luwadi da madigo a nahiyar da har yanzu ake ganin hakan a matsayin mummunan laifi? To, masu fafutuka dai na sa ran hakan.

Suna tunanin cewa zai iya kawo babban sauyi kan wannan halayya a nahiyar.

A takaice dai, akwai yiwuwar ya yi jawabi sosai a kan hakkokin 'yan luwadi da madigo.

5. Hana daukar ciki

Hakkin mallakar hoto
Image caption Akwai yiwuwar Paparoma ya yi jawabi a kan harmta hanyoyin hana daukar ciki

Paparoma ya taba cewa ba lallai ba ne mabiya darikar katolika su dinga haihuwa kamar beraye ba, kafin daga baya fadar Vatican ta fayyace abin da yake nufi da kalaman nasa, inda ta ce ba wai yana magana ne a kan masu iyalai da yawa ba.

Kazalika, hukumomin bayar da agaji na duniya da dama za su so cocin Roman Katolika ya ki bayar da hadin kai wajen amfani da hanyoyin hana daukar ciki na jabu, musamman haramta amfani da kwaroron roba, domin taimakawa mutane a nahiyar da cutar HIV da Aids suka zama babbar matsala.

Ana sa rana Paparoma Francis zai gana da mutane masu dauke da cutar HIV.

Mabiya darikar katolika da dama na kokarin tabbatar da cewa Afrika ta zamo wani bangare mai muhimmanci ga cocin.

A takaice dai, akwai yiwuwar ya soke haramcin da darikar katolika ta sanya na amfani da hanyoyin hana daukar ciki.