Paparoma ya isa kasar Kenya

Image caption Dubban mutane ne ke shirin tarben Paparoma.

A ranar Laraba ne Paparoma Francis ya isa kasar Kenya a ziyararsa ta farko a nahiyar Afirka tun da ya zama Paparoma.

Shugaban kasar Uhuru Kenyatta da 'yan kasar da dama ne suka tarbe shi a filin jiragen saman da ke Nairobi.

Wata kungiya ta 'yan-ba-ruwanmu-da-addini ta ce za ta kai gwamnatin kasar kara a kotu saboda matakin da gwamnatin ta dauka na bai wa 'yan kasar hutu ranar Alhamis domin karrama Paparoman.

Wani babban malamin Musulinci ya yi maraba da ziyarar Paparoman, yana mai cewa za ta "sanyaya zuciyar marasa galihu".

Kasar Kenya dai na da mabiya darikar Katolika da dama wadanda suka sadaukar da rayuwarsu ga koyarwar Cocin ta Katolika.

Yanzu haka wasu 'yan kasar Kenya sun kasa daukar matsaya a kan wasu batutuwa da ake ta cece-kuce a kansu da suka hada da amfani da magungunan hana daukar ciki na zamani.

Cocin dai tana matukar adawa da batun shan magungunan amma wasu kungiyoyin farar hula suna shelar yin amfani da su.

Ana dai sa san ziyarar ta Paparoma ka iya chanja al'amura a kasar.