Shin 'yan ta'adda za su yi nasara?

Hakkin mallakar hoto Getty Images

A yayin da Turai ta ke fama da matsalar tsaro bayan harin da aka kai Paris, ana ci gaba da tattauna wa a kan 'ta'addancin wannan zamani.

Akwai darusa da dama a tarihin ta'addanci a cewar Benedict Wilkinson.

Johann Most ba kyakyawan mutum ba ne. An haife shi a shekarun 1940, cutar sanyi ta kama kumatun shi na gefen hagu a lokacin ya na yaro.

Cutar ta yi tsanani har sai da aka yi masa tiyata aka cire barin habarsa wanda hakan ya sa halittar fuskarsa ta yi muni kuma hakan ke sanya shi shi yawan yin fushi da saurin jin haushi.

Tiyatar da aka yi masa ta saka shi yana ganin kamar shi bare ne har tsawon yarintarsa, amma kuma daga nan sai Most ya samu aikin hada bangon littafi, kuma hakan ya sa ya yi tafiye-tafiye zuwa Turai inda ya dinga shafe lokacinsa wajen yin rubuce-rubuce a kan kwaminisanci da siyasa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

A shekarun 1870, ya yi fice a tsakanin kwaminisanci ba kawai don abubuwan da ya ke yi ba, sai dai saboda litaffin Marx Das Kapital da ya takaita.

Ko da yake a cikin 'yan shekaru masu zuwa, tsatsauran ra'ayin Most ya wuce na Marx ma.

Ya fice daga kwaminisawa ya zama mai tsananin tayar da rikici kuma baya son bin doka.

Ya na ganin kalamai da jawabai mai yiwuwa suna da rawar da zasu taka amma nasarar kwamisinanci ta dogara ne a kan amfani da tashin hankali.

Akasarin mutane sun yi la'akari da cewar abinda ake bukata shi ne juyin juya hali na tashin hankali.

Idan aka yi gaba shekaru 125, abin ya sha bamban saboda wannan mutumin daban ne kuma mai burin siyasa daban.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Abu Mus'ab kyakyawa ne kuma an haife shi a al-Suri a Aleppo a shekarar alif 1958.

Kamar mutane da dama, al-Suri ya gano babbar matsala a yin amfani da ta'addanci a matsayin dabarun cimma muhimman bukatun siyasa.

Ya ce, ta'addanci zai iya fusata al'ummomi da gwamnatoci, amma kuma ba abu bane da ya isa ya yi musu wata barazana a zahirance.

Gwamnatoci suna da karfi kuma tsare-tsaren siyarsa su na jurewa ta'addanci.

Ta'addanci zai iya jawo munmunar halaka da asara mai muni, amma kuma ga al-Suri wannan bai isa ya ragewa gwamnati karfin iko ko kuma ya tilasta mata canza manufofin da ta ke dauka da muhimmanci.

A don haka, al-Suri ya kirkiri wani sabon shiri wanda ya ke ganin zai samar da wata kungiya ta duniya gaba daya a bisa gamammiyar akida wacce kuma fito-na-fito ke da muhimmanci gare ta.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Akwai dalilai biyu na rikici. Da farko ya ce ta'addanci yana matsayin wani nau'i na Farfaganda ta inda ya ke jawo magoya baya da kuma wadanda su ka yarda da hakan, kamar yadda da dama suka gani.

Wannan ya kai mu ga mataki na biyu, a lokacin da mutanen da kungiyar ta cika ta batse da magoya bayanta da masoyanta, zasu iya maimaita abubuwa na rikici.

A yayin da wadannan rikice-rikice zasu iya zama marasa karfi wadanda ba a shirya yinsu ba, a ganin al-Suri bazuwar irin wadannan rikice-rikicen zai iya saka mutane su rika dari-dari kuma ya haifar da tsoro.

Zasu ci karfin gwamnati ta yadda zata mika wuya. Duk wadannan labaran suna nuna babbar matsalar da ke tattare da ta'addanci - abin da ake kira - wani yanayi na an gudu ba tsira ba na 'yan ta'adda.

Kuma a lokuta da dama 'yan ta'addan suna so su kawo sauyi a siyasa, amma kuma basu da karfin cimma burinsu.

Akwai wawakeken gibi tsakanin abinda su ke da shi da kuma wanda su ke bukata.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

A tarihin ta'addanci, wannan sarkakiyar ta kawo dabaru da dama.

Kungiyar IS sun yi kokarin mamayar yakuna ta hanyar karfin tuwo.

Kamar harin da aka kai Paris a baya-bayan nan da barazanar rikici a Turai, sun bayyana sabon buri a kan duniya gaba daya.

Wasu da dama da al- Suri sun yi kokarin shawo kan sarkakiyar 'yan ta'adda ta wasu hanyoyin - ta hanyar yake-yake, da kuma jawo mutane na jiki.

Duk da wadannan abubuwan, a gano cewar ta'addanci wata hanya ce da marasa karfi ke amfani da ita wajen fin karfin masu karfi.

Sai dai a wani bangaren kuma 'yan ta'adda basu da isasshiyar dukiyar da suke yaki da ita amma suna da akida mai tsauri da kuma wasu burikansu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images