Boko Haram: An kashe mutane 16 a Bosso

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Har yanzu babu cikakken bayani kan harin.

Mazauna garin Gogole da ke Bosso a Jamhuriyar Nijar sun shaida wa BBC cewa 'yan Boko Haram sun kai hari a garin ranar Laraba da daddare.

Sun kuma ce ba-ta-kashin da aka yi tsakanin mayakan kungiyar Boko Haram da 'yan kato-da-gora a garin, ya yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane 16.

Har yanzu dai babu cikakken bayani kan yadda lamarin ya auku.

Kungiyar ta Boko Haram ta tsananta kai hare-hare a Bosso da wasu yankuna na Jamhuriyar Nijar tun daga farkon wannan shekarar, inda aka sanaya dokar ta-baci a yankin Diffa.

Shugabannin kasashen da ke yankin Tafkin Chadi sun kafa rundunar da za ta murkushe mayakan kungiyar ta Boko Haram, sai dai har yanzu kungiyar na ci gaba da kai hare-hare.

Ko da a farkon makon nan, sai da gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta soke bikin nunin tufafin gargajiya da ake yi a Yamai a duk shekara saboda fargabar hare-haren 'yan BokoHaram.