'Bello Chindo ba dan Boko Haram ba ne'

Jamian tsaron Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jamian tsaron Najeriya

Iyalan daya daga cikin mutanen da hukumomin tsaron Nijeriya suka kama a baya-bayan nan da ake zargi da kasancewa babban dan kungiyar Boko Haram sun musanta zargin da ake yi masa .

A kwanakin baya ne jami'an tsaro suka kama Bello Chindo a filin jirgin sama na Abuja, inda suka ce yana cikin 'yan Boko Haram su 100 da aka fi nema ruwa-a-jallo, wadanda aka wallafa hotunansu.

Sai dai 'yan-uwansa sun ce a iya saninsu babu ma hotonsa a cikin hotunan mutanen da ake nema.

Sun yi kira ga hukumomin Najeriya su sake shi, suna masu cewa bai kamata a ci gaba da tsare shi ba.