IS: Cameron ya nemi agajin 'yan majalisar Biritaniya

Image caption Cameron ya ce zai nemi 'yan majalisar dokokin su kada kuri'a kan kai wa IS hari.

Firai Ministan Biritaniya David Cameron ya gabatar da bukatar ganin kasarsa ta kaddamar da hare-hare ta sama a kan maboyar 'yan kungiyar IS a Syria.

Mista Cameron ya fada wa majalisar dokoki da ta cika makil cewa, ba daidai ba ne a yi zaton Biritaniya ta koma gefe guda tana kallo yayin da wasu kasashen suka tashi tsaye wajen yaki da 'yan kungiyar IS.

David Cameron ya ce hare-haren ta sama wani bangare ne na gagarumin shirin dakile musabbabin kai hare-haren tun daga tushe.

Ya kara da cewa zai bukaci 'yan majalisar dokokin su kada kuri'a kan ba shi goyon baya domin yaki da IS idan ya tabbatar zai samu goyon bayan 'yan majalisar.

A kwanakin baya, wani kwamitin majalisar dokokin ya yi gargadin cewa bai kamata sojin kasar su ci gaba da kai hare-hare a kan kungiyar IS a Syria ba, sai sun tabbatar kasashen duniya sun samar da hanyar da za a bi a murkushe kungiyar.