'Auren wuri' zai rubanya — UNICEF

Hakkin mallakar hoto au
Image caption Kungiyar Tarayyar Afirka na yin taro kan yadda za a magance matsalar auren wuri.

Asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya ya ce adadin yara mata da a kan aurar da wuri zai rubanya nan da shekaru 35 a nahiyar Afirka.

Asusun ya ce adadin zai kai miliyan 310 a shekarar 2050.

UNICEF ya yi wannan bayani ne a daidai lokacin da kungiyar tarayyar Afrika ke fara taron kwanaki biyu a kasar Zambia domin kawo karshen auren wurin a Afrika.

An dai kiyasta cewa akwai mace daya a cikin mata uku da iyayenta ko sarakunan gargajiya ke yi musu auren wuri kafin su cika shekaru 18.