Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu za su yi taro

Hakkin mallakar hoto Reuters

Jami'ai daga Korea ta arewa da Korea ta kudu za su yi wani taro da ba kasafai aka saba ganin irinsa ba, kusan irinsa na farko da gwamnatocin biyu suka hadu domin tattaunawa wajen warware rikicin da ke tsakanin kasashen biyu.

A na gab da fara taron ne a kauyen Panmunjom da ke yankin Korea ta arewa.

Wakilin bbc ya ce wani abu mai muhimmanci shi ne cewa a na taron ne cikin rashin yarda da amince wa da juna.

Ana ganin watakila tattaunawar ba za ta haifar da wani abin a zo agani ba.