Kogi: PDP za ta yi karar INEC

Image caption Abubakar Audu shi ne dan takarar gwamna na Kogi karkashin jam'iyyar APC, ya rasu ranar Lahadi

Jam'iyyar PDP a Najeriya ta ce za ta kai karar hukumar zaben kasar, INEC, sakamakon hukuncin da hukumar ta zartas na bai wa jam'iyyar APC damar tsayar da sabon dan takarar gwamna a jihar Kogi.

PDP ta bayyana haka ne bayan taron majalisar gudanarwar jam'iyyar na ranar Laraba a Abuja.

Jami'iyyar ta ce za ta kai karar ne nan da kwanaki kadan masu zuwa, tana mai cewa kundin tsarin mulkin kasar bai kunshi dokar da ta ce za a iya maye gurbin dan takarar da ya mutu ba, bayan da aka riga aka fara kirga kuri'a.

Jam'iyyar ta kara da cewa INEC ba ta da wani zabi da ya wuce ta sanar da dan takarar gwamnan Kogi a karkashin jam'iyyar PDP wanda kuma shi ne gwamnan jihar, a matsayin wanda ya yi nasarar lashe zaben jihar.

A ranar Asabar din da ta gabata ne aka gudanar da zaben gwamann jihar Kogi kuma INEC ta ce zaben bai kammalu ba sai an sake a mazabu 91.

Amma a ranar Lahadi sai Allah ya yi wa dan takarar karkashin jam'iyyar APC Alhaji Abubakar Abdu rasuwa, wanda kuma shi ne ke kan gaba da yawan kuri'u.