PDP ta ce za ta garzaya kotu kan zaben Kogi.

Shugabannin Jam'iyyar adawa ta PDP sun ce za su garzaya kotu domin kalubalantar matakin da hukumar zabe ta dauka na ba wa jam'iyyar APC mai mulki damar ta fitar da sabon dan takara a zaben gwamnan jihar Kogi.

Dan takarar jam'iyyar APC a zaben, Abubakar Audu ya rasu ne a dai-dai lokacin da ake kidaya kuri'un zaben da hukumar zabe ta ce za a kammala shi ranar biyar ga watan Disamba mai zuwa.

A don haka hukumar zabe ta ce jam'iyyarsa za ta iya sauya dan takara a kuma karasa zaben.

Sai dai Jam'iyyar PDPn ta ce matakin na hukumar zabe ya saba da dokokin kasar.

Ta ce dan takarar ta ya kamata a bayana a matsayin wanda ya nasara a zaben.