Rasha za ta sanya wa Turkiya takunkumi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce Turkiyya ba ta gargadi jirgin Rasha ba kafin ta harbo shi

Rasha na shirin sanya wa Turkiyya jerin takunkumin tattalin arziki sakamakon harbo jirgin yakinta da aka yi a kan iyakar Turkiya da Syria.

Firai ministan Rasha Dmitry Medvedev, ya ce matakan za su iya hada wa da dakatar da shirye-shiryen hadin gwiwa na zuba jari.

Ya ce yana fatan karbar jerin takunkuman a rubuce nan da kwanaki biyu masu zuwa.

Turkiyya ta fitar da wata murya da aka nada, wadda ta kira gargadin da ta yi wa jirgin yakin Rasha samfurin SU-24 kan ka da ya keta sararin samaniyarta.

Yayin da Rasha kuwa ta ce an harbo jirgin ne ba tare da wani gargadi ba, a yayin da yake kai hare-hare ta sama a Syria ranar Talata.