An kulle ma'aikata saboda latti

Hakkin mallakar hoto Reuters

An kulle wasu ma'aikata guda 20 a kasar Tanzania saboda sun yi latti wajen zuwa wani taro.

Kwamishinan yankin Kinondoni a babban birnin Tanzanian, Dar es Salam ne ya bayar da umurnin a kama ma'aikatan da suka yi lattin sa'oi 3 wajen halartar taron.

Lamarin ya faru ne bayan shugaban gundumar ya kira taron domin ya warware wata takkadama da aka dade ana yi a kan wani fili a yankin.

'Yan kasar dai da dama na yin korafi cewar ma'aikatan gwamnati suna dadewa idan suka tafi hutawa a ranakun aiki.