Paparoma zai tuna da kiristocin da aka kashe

Image caption Paparoma Francis

Fafaroma Francis zai yi addu'o'i ga wasu kiristocin kasar Uganda da aka kashe sakamakon sadaukar da rayuwarsu ga addini a karni na 19, a ziyarar da ya ke yi yanzu a Afirka.

Kimanin mutane miliyan biyu ne ake sa ran zasu halarci taron addu'o'i a Namugongo, inda aka kona akasarin kiristocin 45 mabiya darikun Anglikan da Katoloka da ransu.

Addu'ar tazo ne a daidai lokacin da ake cika shekaru 50, da mujami'ar Katolika ta bayyana mamatan a matsayin wadanda suka yi shahada.

Tun da farko, Fafaroma Francis ya ce yana so ne ya janyo hankalin duniya zuwa nahiyar Afirka.

A gobe Lahadi ne Fafaroma Francis din zai wuce jamhoriyar Afirka ta Tsakiya, inda anan ne zai karkare ziyarar tasa a Afirka da yake yi yanzu.