'Saudiyya na shirin fille kan mutane 50'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Amnesty ta ce Saudiyya ta yanke hukuncin kisa ga mutane 151 a wannan shekarar kadai.

Kungiyar kare hakkin bil adama, Amnesty International ta ja hankalin al'umma game da rahotannin da ke cewa hukumonin Saudiyya na shirin yanke hukuncin kisa kan mutane da dama a rana guda.

Jaridar Okaz ta ce mutane 55 ne da ake zargi da aikata laifukan ta'addanci ke jiran wannan hukunci, amma wata jaridar mai suna al-Riyadh ta ce mutane 52 ne.

A cikin wadanda za a yanke wa hukuncin har da mabiya Shi'a wadanda suka yi zanga-zangar adawa da gwamnati.

Amnesty ta ce ganin yadda yanke hukuncin kisa ya karu a kasar a bana, dole ta dauki rahoton da muhimmanci.

Kungiyar ta ce a kalla mutane 151 aka kashe a Saudiyya a wannan shekarar, wanda ba a taba samun yawan hakan ba tun shekarar 1995.